4 In kuma ya dace in tafi, to, sai su tafi tare da ni.
4 In ya kyautu ni ma in tafi, to, sai su raka ni.
Ba kuwa haka kaɗai ba, har ma ikkilisiyoyi sun zaɓe shi yă riƙa tafiya tare da mu kan wannan aikin alheri da muke yi saboda ɗaukakar Ubangiji, da kuma nuna kyakkyawar niyyarmu.
sun roƙe mu sosai don su sami damar yin bayarwa a wannan hidima ga tsarkaka.
Yanzu kam, ina hanyata zuwa Urushalima don in kai gudummawa ga tsarkaka a can.
In kuwa na iso sai in ba da wasiƙun gabatarwa ga mutanen da kuka amince da su, in kuma aike su da taimakonku zuwa Urushalima.
Bayan na zazzaga Makidoniya, zan zo wurinku, domin zan ratsa ta Makidoniya.