Duk lokacin da za ku tafi yaƙi a ƙasarku, in akwai waɗansu da suke matsa muku, za ku yi amfani da waɗannan kakaki ta wurin hura su, alama ce, cewa za a je yaƙi. Sa’an nan Ubangiji Allahnku zai tuna da ku, yă cece ku daga maƙiyanku.
Azabana, azabana! Ina birgima cikin zafi. Azabana, azabar zuciyata! Zuciyata yana bugu a cikina, Ba zan yi shiru ba. Gama na ji karan ƙaho; na ji kirarin yaƙi.
Ku busa ƙaho a cikin Sihiyona; ku yi karar amo a tsaunina mai tsarki. Bari dukan mazaunan ƙasar su yi rawan jiki, gama ranar Ubangiji tana zuwa. Tana gab da faruwa
Kuma a wannan rana zai busa ƙaho mai kāra sosai. Waɗanda suke mutuwa a Assuriya da kuma waɗanda aka kai zaman bauta a Masar za su zo su kuma yi wa Ubangiji sujada a dutse mai tsarki a Urushalima.
Abubuwan nan marasa rai ma da sukan yi ƙara, kamar su algaita ko molo, in muryarsu ba tă fita sosai ba, yaya wani zai san abin da ake busawa ko kaɗawa?