Yanzu kam muna ganin abubuwa kamar a madubi sai dai ba sosai ba, amma a ranan nan za mu gani fuska da fuska. Yanzu kam sanina ba cikakke ba ne, amma a ranan nan zan kasance da cikakken sani, kamar dai yadda Allah ya san ni a yanzu.
Sa’an nan wata zai ruɗe, rana ta ji kunya; gama Ubangiji Maɗaukaki zai yi mulki a kan Dutsen Sihiyona da kuma a cikin Urushalima, da kuma a gaban dattawanta, da ɗaukaka.
Ba cewa na riga na sami dukan wannan ba ne, ko kuma an riga an mai da ni cikakke ba, sai dai ina nacewa don in kai ga samun abin da Kiristi Yesu ya riƙe ni saboda shi.