A cikin ikkilisiya, da farko dai Allah ya zaɓa waɗansu ya naɗa su su zama manzanni, na biyu annabawa, na uku malamai, sa’an nan masu yin ayyukan banmamaki, sai masu baiwar warkarwa, da masu taimakon waɗansu, da masu baiwar gudanarwa, sa’an nan kuma masu magana da harsuna iri-iri.
Saboda haka Kiristi kansa ya ba wa waɗansu baiwa su zama manzanni, waɗansu su zama annabawa, waɗansu su zama masu wa’azi, waɗansu kuma su zama fastoci, da kuma malamai.