Sun sa ni kishi ta wurin abin da ba allah ba, suka kuma husata ni da gumakansu na wofi. Zan sa su yi kishi ta wurin waɗanda ba mutane ba; zan sa su yi fushi ta wurin al’ummar da ba ta da sani.
Azurfarsu ko zinariyarsu ba za su iya cetonsu ba a ranar fushin Ubangiji.” A cikin zafin kishinsa za a hallaka dukan duniya gama zai kawo ƙarshen dukan mazaunan duniya nan da nan.
“Kaitonka mai gardama da Wanda ya yi ka, da wanda yake kasko a cikin kasko a ƙasa. Yumɓu ya iya ce wa magini, ‘Me kake yi?’ Aikinka na iya cewa, ‘Ba shi da hannuwa’?
Ba za ka durƙusa gare su, ko ka yi musu sujada ba. Gama ni, Ubangiji Allahnka mai kishi ne, nakan hukunta ’ya’ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina,
Me ya sa kuka tsokane ni in yi fushi saboda abin da hannuwanku suka yi, kuna ƙone turare wa waɗansu alloli a Masar, inda kuka zo don ku zauna? Za ku hallakar da kanku ku kuma mai da kanku abin la’ana da abin zargi da abin ba’a a cikin dukan al’umman duniya.