In wani ya yi magana, ya kamata yă yi ta a matsayin wanda yake magana ainihin kalmomin Allah. In wani yana yin hidima, ya kamata yă yi ta da ƙarfin da Allah ya tanadar, domin a cikin kome a yabi Allah ta wurin Yesu Kiristi. A gare shi ɗaukaka da iko sun tabbata har abada abadin. Amin.
Sa’an nan na ji kowace halitta a sama da ƙasa da ƙarƙashin ƙasa da kuma bisan teku, da kome da yake cikinsu yana rerawa, “Gare shi mai zama a kan kursiyin da kuma ga Ɗan Ragon yabo da girma da ɗaukaka da iko, sun tabbata har abada abadin!”