Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Zefaniya 3:9 - Littafi Mai Tsarki

9 “Sa'an nan zan sauye harshen mutane da harshe mai tsabta, Domin dukansu su yi kira ga sunan Ubangiji, Su kuma bauta masa da zuciya ɗaya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 “Sa’an nan zan tsarkake leɓunan mutanen, don dukansu su kira bisa ga sunan Ubangiji su kuma yi masa hidima kafaɗa da kafaɗa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Zefaniya 3:9
21 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A lokacin, harshen mutanen duniya ɗaya ne, maganarsu kuma ɗaya ce.


A wannan rana, za a yi amfani da harshen Ibrananci a birane biyar na Masar. Mutanen da suke can za su riƙa yin rantsuwarsu da sunan Ubangiji Mai Runduna. Za a sa wa ɗaya daga cikin biranen nan suna, “Birnin Hallaka.”


Dukan al'ummai za su tuna da Ubangiji, Za su zo gare shi daga ko'ina a duniya, Dukan kabilai za su yi masa sujada.


“A wannan rana al'umman duniya da yawa za su haɗa kai da Ubangiji, za su kuwa zama jama'ata, ni kuma zan zauna a tsakiyarki. Za ki sani Ubangiji Mai Runduna ya aike ni gare ki.


Duniya za ta cika da sanin ɗaukakar Ubangiji, Kamar yadda ruwa ya cika teku.


Kada wata alfasha ta fita daga bakinku, sai dai irin maganar da ta kyautu domin ingantawa, a kuma yi ta a kan kari, domin ta sa alheri ga masu jinta.


Mutumin kirki kam, ta kyakkyawar taskar zuciya tasa yakan yi abin kirki, mugu kuwa, ta mummunar taskar zuciya tasa yakan yi mugun abu.


A ranar, Ubangiji zai zama Sarkin Duniya duka, zai kuma zama shi ne Ubangiji shi kaɗai, ba wani suna kuma sai nasa.


Sa'an nan mala'ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji waɗansu muryoyi masu ƙara a Sama, suna cewa, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Almasihunsa, shi kuma zai yi mulki har abada abadin.”


Ubangiji zai tsananta musu, Zai kawo wa dukan gumakan da yake a duniya yunwa. Kowane mutum a duniya zai yi masa sujada a inda yake, Har da ƙasar sauran al'umma.


“Ya Ubangiji, ƙarfina da kagarata, Mafakata a ranar wahala, A gare ka al'ummai za su zo, Daga ƙurewar duniya, su ce, ‘Kakanninmu ba su gāji kome ba, sai ƙarya, Da abubuwan banza marasa amfani.’


Daga gabas zuwa yamma a yabi sunan Ubangiji!


Ga Shitu kuma aka haifi ɗa, ya kuwa raɗa masa suna Enosh. A wannan lokaci ne mutane suka fara kira bisa sunan Ubangiji.


Salama, salama,” in ji Ubangiji, “Ga wanda yake nesa da wanda yake kusa. Zan warkar da su.


Ya taɓa leɓunana da garwashin wutar ya ce, “Wannan ya taɓa leɓunanka, yanzu fa an kawar da laifofinka, an kuma gafarta maka zunubanka.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ