Zefaniya 3:14 - Littafi Mai Tsarki14 Ki raira waƙa da ƙarfi, ya ke Sihiyona! Ki ta da murya, ya Isra'ila! Ki yi murna, ki yi farin ciki, Ya ke Urushalima! အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202014 Ki rera, ya Diyar Sihiyona; ki tā da murya, ya Isra’ila! Ki yi murna ki kuma yi farin ciki da dukan zuciyarki, Ya Diyar Urushalima! အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
za a sāke jin muryar murna da ta farin ciki, da muryar ango da ta amarya, da muryoyin mawaƙa, sa'ad da suke kawo hadayun godiya a cikin Haikalin Ubangiji, suna cewa, “ ‘Ku yi godiya ga Ubangiji Mai Runduna, Gama Ubangiji nagari ne, Gama madawwamiyar ƙaunarsa tabbatacciya ce.’ “Gama zan mayar da arzikin ƙasar kamar yadda yake a dā, ni Ubangiji na faɗa.”