Zan ƙarfafa hannun Sarkin Babila, in sa takobina a hannunsa, amma zan karya hannuwan Fir'auna, zai yi nishi a gaban Sarkin Babila, kamar mutumin da aka yi wa raunin ajali.
Sa'ad da aka ci Ashdod, sai Ubangiji ya ce, “Bawana Ishaya ya yi ta yawo tsira, ba kuma takalmi a ƙafarsa har shekara uku. Wannan ita ce alamar abin da zai faru a ƙasa Masar da Habasha.