Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Zefaniya 1:17 - Littafi Mai Tsarki

17 “Zan aukar wa mutane da wahala, Za su kuwa yi tafiya kamar makafi, Domin sun yi wa Ubangiji zunubi. Za a zubar da jininsu kamar ƙura, Namansu kuwa kamar taroso.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 “Zan kawo baƙin ciki a kan mutane za su kuma yi tafiya kamar makafi, domin sun yi wa Ubangiji zunubi. Za a zubar da jininsu kamar ƙura kayan cikinsu kuma kamar najasa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Zefaniya 1:17
41 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Duniya kuwa za ta zama kufai, Saboda mazaunan da suke cikinta, Saboda hakkin ayyukansu.


Tun da ka ce, kai mai arziki ne, cewa ka wadata ba ka bukatar kome, ba ka sani ba kuwa kai ne matsiyacin, abin yi wa kaito, matalauci, makaho, tsirara kuma.


Waɗanda aka kora a Endor, Gawawwakinsu kuwa suka ruɓe a ƙasa.


Mai ƙin ɗan'uwansa kuwa, a duhu yake, a cikin duhu yake tafiya, bai san ma inda yake sa ƙafa ba, domin duhun ya makantar da shi.


Domin duk wanda ya rasa halayen nan, to, makaho ne ko kuwa ganinsa dishi-dishi ne, ya kuma mance an tsarkake shi daga zunubansa na dā.


'Yan'uwa, ga wata asirtacciyar gaskiya da nake so ku sani, domin kada ku zaci ku masu hikima ne, taurarewar nan–wadda ba mai tabbata ba ce–ta sami Isra'ilawa ne, har adadin al'ummai masu ɗungumawa zuwa ga Allah ya cika.


To, yaya ke nan? Ashe, abin da Isra'ila take nema, ba su samu ba ke nan, amma zaɓaɓɓun nan sun samu, sauran kuwa sun taurare.


Ƙyale su kawai, makafin jagora ne. In kuwa makaho ya yi wa makaho jagora, ai, duk biyu sai su faɗa a rami.”


“Na aukar muku da annoba irin wadda na aukar wa Masar. Na karkashe samarinku a wurin yaƙi, Na kwashe dawakanku. Na cika hancinku da ɗoyin sansaninku. Duk da haka ba ku komo wurina ba.


Yara da tsofaffi suna kwance cikin ƙurar tituna, An kashe 'ya'yana, 'yan mata da samari, da takobi. Ka kashe su a ranar fushinka, ba tausayi.


“Abin da Ubangiji ya yi daidai ne, Gama ni na ƙi bin maganarsa, Ku ji, ya ku jama'a duka, Ku dubi wahalata, 'Yan matana da samarina, An kai su bauta!


“Ubangiji ya tattara laifofina Ya yi karkiya da su, Ya ɗaura su a wuyana, Ya sa ƙarfina ya kāsa. Ya kuma bashe ni a hannun Waɗanda ban iya kome da su ba.


Urushalima ta yi zunubi ƙwarai da gaske, Saboda haka ta ƙazantu, Dukan waɗanda suka girmama ta sun raina ta Domin sun ga tsiraicinta, Ita kanta ma tana nishi, ta ba da baya.


Saboda haka ka kawo wa 'ya'yansu yunwa, Ka bashe su ga takobi, Bari matansu su rasa 'ya'ya, mazansu su mutu, Ka sa annoba ta kashe mazansu, A kashe samarinsu da takobi a yaƙi.


Zan sa musu masu hallakarwa huɗu, in ji Ubangiji, “da takobi don kisa, da karnuka don yayyagawa, da tsuntsayen sararin sama, da dabbobin duniya don su cinye, su hallakar.


Gama haka Ubangiji ya ce, “Ga shi, ina jefar da mazaunan ƙasar daga ƙasarsu a wannan lokaci, Zan kawo musu wahala, za su kuwa ji jiki.”


“Al'amuranki da ayyukanki suka jawo miki wannan halaka, Tana da ɗaci kuwa, Ta soki har can cikin zuciyarki.”


Muguntarka za ta hore ka, Riddarka kuma za ta hukunta ka. Sa'an nan za ka sani, ka kuma gane, Ashe, mugun abu ne, mai ɗaci, a gare ka Ka rabu da Ubangiji Allahnka, Ba ka tsorona a zuciyarka. Ni Ubangiji, Allah Mai Runduna na faɗa.”


Ya Isra'ila, kai ne ka jawo wa kanka wannan, Da ka rabu da Ubangiji Allahnka, Sa'ad da ya bishe ka a hanya.


Ubangiji ya ce, “Kuna tsammani na kori mutanena Kamar yadda mutum yakan saki mata tasa? To, in haka ne ina takardar kisan auren? Kuna tsammani na sayar da ku cikin bauta Kamar mutumin da ya sayar da 'ya'yansa? A'a, kun tafi bauta ne saboda da zunubanku, Aka tafi da ku saboda da laifofinku.


Ubangiji ya sa ku ku yi gyangyaɗi ku yi barci mai nauyi. Annabawa ne ya kamata su zama idon jama'a, amma Allah ya rufe idanunsu.


Su ne marasa ba da gaskiya, waɗanda sarkin zamanin nan ya makantar da hankalinsu, don kada hasken bisharar ɗaukakar Almasihu, shi da yake surar Allah, ya haskaka su.


Za a shimfiɗa su a rana, da a farin wata, da a gaban dukan rundunan sama, waɗanda suka ƙaunata, suka bauta wa, waɗanda suka nemi shawararsu, suka yi musu sujada. Ba za a tattara su a binne ba, amma za su zama juji a bisa ƙasa.


Zan hukunta ki kamar yadda akan hukunta mata waɗanda suka ci amanar aure, suka zub da jini. Zan hallaka ki cikin zafin fushina da kishina.


Gama jinin da ta zubar yana tsakiyarta, Ta zubar da shi a kan dutse, Ba ta zubar da shi a ƙasa inda za ta rufe shi da ƙura ba.


Don a tsokani fushina har in yi sakayya, Na zuba jinin da ta zubar a kan dutse, Don kada a rufe shi.’


Bari mu kwanta mu sha kunyarmu, bari kuma rashin kirkinmu ya rufe mu. Gama mun yi wa Ubangiji Allahnmu zunubi mu da kakanninmu, tun daga ƙuruciyarmu har zuwa yau, ba mu yi biyayya ga maganar Ubangiji Allahnmu ba.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ