Zakariya 9:9 - Littafi Mai Tsarki9 Ki yi murna ƙwarai, ya Sihiyona! Ta da murya ya Urushalima! Ga Sarkinki yana zuwa wurinki, Shi mai adalci ne, mai nasara, Shi kuma mai tawali'u ne, Yana bisa kan jaki, a kan aholaki. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20209 Ki yi murna ƙwarai, ya Diyar Urushalima! Ki yi sowa, Diyar Urushalima! Duba, ga sarkinki yana zuwa wurinki, mai adalci yana kuma da ceto, mai tawali’u yana kuma hawan jaki, yana a kan ɗan aholaki, a kan ’yar jaka. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Wannan shi ne jawabin da Allah ya yi a kan dabbobin da suke kudancin hamada, “Jakadu sun yi tafiya a ƙasa mai hatsari, inda zakoki suke, inda macizai masu dafi da macizai masu tashi sama suke. Suna labta wa jakunansu da raƙumansu kayayyaki masu tsada da za su kai gaisuwa ga al'ummar da ba za ta taimake su da kome ba.