Haka nan ku masu ƙuruciya, ku yi biyayya ga dattawan ikkilisiya. Dukanku ku yi wa kanku ɗamara da tawali'u, kuna bauta wa juna, gama “Allah yana gāba da masu girmankai, amma yana wa masu tawali'u alheri.”
Yanzu ni, Nebukadnezzar, ina yabon Sarkin Samaniya, ina ɗaukaka shi, ina kuma girmama shi saboda dukan ayyukansa daidai ne, al'amuransa kuma gaskiya ne. Yakan ƙasƙantar da masu girmankai.”
Mulkin Isra'ila ya ƙare, darajarsa tana dushewa kamar rawanin furanni a kan shugabanninsa da suka bugu da giya. Sun bulbula turare a kawunansu na girmankai, amma ga su nan a kwance bugaggu.
Ubangiji Mai Runduna ne ya shirya wannan! Ya shirya haka ne don ya kawo ƙarshen girmankanta saboda abin da suka aikata, don ya ƙasƙantar da manyan mutanenta.
Allah yakan ba wani mutum dukiya, da daraja, da wadata, i, da kowane abu da yake bukata. Amma bai ba shi iko ya more su ba. A maimakonsa wani baƙo ne zai more su. Wannan aikin banza ne ba kuwa daidai ba ne.
Ubangiji ya ce, “Ashkelon za ta gani ta ji tsoro, Gaza kuma za ta yi makyarkyata da azaba, Haka kuma Ekron za ta fid da zuciya, Sarki zai halaka cikin Gaza, Ashkelon za ta zama kufai.
Zan kawar da jininsu daga bakinsu, Da kuma haramtattun abubuwa daga haƙoransu. Sauransu za su zama jama'ar Allahnmu, Za su zama kamar sarki cikin Yahuza. Mutanen Ekron za su zama kamar Yebusiyawa.