Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Zakariya 8:9 - Littafi Mai Tsarki

9 “Ni Ubangiji Mai Runduna na ce, ku himmantu, ku da kuke jin magana ta bakin annabawa a waɗannan kwanaki tun lokacin da aka ɗora harsashin ginin Haikalin Ubangiji Mai Runduna, don a gina Haikalin.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Ku da yanzu kuke jin maganan nan da annabawa suka faɗi, waɗanda suke a nan lokacin da aka kafa harsashin haikalin Ubangiji Maɗaukaki, bari hannuwanku su zama da ƙarfi don a gama gina haikalin.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Zakariya 8:9
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ku faɗa wa dukan wanda ya karai, ku ce, “Ka ƙarfafa, kada kuwa ka ji tsoro! Allah yana zuwa domin ya kuɓutar da kai, Yana zuwa domin ya ɗauki fansa a kan abokan gābanka.”


“Ka faɗa wa Zarubabel, mai mulkin Yahuza cewa, ‘Ina cikin shirin girgiza sammai da duniya.


Za ka arzuta idan ka kula ka kiyaye dokoki da ka'idodi da Ubangiji ya umarci Musa saboda Isra'ila. Ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin hali. Kada ka ji tsoro, kada kuma ka karaya.


Saboda haka, ya kai ɗana, sai ka ƙarfafa da alherin da yake ga Almasihu Yesu.


A ƙarshe kuma, ku ƙarfafa ga Ubangiji, ga ƙarfin ikonsa.


Ubangiji Mai Runduna ya yi magana da ni, ya ce,


Ya jama'ar Yahuza da jama'ar Isra'ila, kamar yadda kuka zama abin la'antarwa a cikin al'ummai, haka kuma zan cece ku, ku zama masu albarka, kada ku ji tsoro, amma ku himmantu.


Zarubabel ɗan Sheyaltiyel kuwa, da Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist, da dukan sauran mutane, suka yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnsu, suka kuma yi biyayya da maganar annabi Haggai, kamar yadda Ubangiji Allahnsu ya faɗa masa. Mutane kuwa suka yi tsoron Ubangiji.


A rana ta fari ga watan shida a shekara ta biyu ta sarautar sarki Dariyus, Ubangiji ya yi magana da annabi Haggai, cewa ya yi magana da Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, mai mulkin Yahuza, da Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist.


Sarki Dawuda kuma ya ce wa ɗansa Sulemanu, “Ka yi ƙarfin hali, ka dāge sosai, ka kama aikin, kada ka ji tsoro, kada kuwa ka karai, gama Ubangiji Allah, wato Allahna, yana tare da kai. Ba zai bari ka ji kunya ba, ba kuwa zai rabu da kai ba, har ka gama dukan aikin Haikalin.


Kada wannan littafin dokoki ya rabu da bakinka, amma zai zama abin da za ka yi ta tunani a kansa dare da rana domin ka kiyaye, ka kuma aikata bisa ga dukan abin da aka rubuta a ciki, gama ta haka za ka yi albarka cikin hanyarka, ta haka kuma za ka yi nasara.


Ka dāge, ka yi ƙarfin hali, gama kai ne za ka yi jagorar wannan jama'a su mallaki ƙasa wadda na rantse zan ba kakanninsu.


Dattawan Yahuza suka yi nasarar ginin ta wurin wa'azin annabi Haggai da Zakariya ɗan Iddo. Suka gama ginin bisa ga umarnin Allah na Isra'ila, da umarnin Sairus, da Dariyus, da Artashate sarakunan Farisa.


Yanzu ku tuna a ran nan, wato rana ta ashirin da huɗu ga watan tara, tun daga ranar da aka aza harsashin ginin Haikalin Ubangiji.


Amma ku sai ku yi ƙarfin hali, kada ku firgita, gama za a ba ku ladan aikinku.”


Ku ƙarfafa hannuwan da suka gaji, Da gwiwoyin da suke fama da rashin ƙarfi.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ