“A wannan rana al'umman duniya da yawa za su haɗa kai da Ubangiji, za su kuwa zama jama'ata, ni kuma zan zauna a tsakiyarki. Za ki sani Ubangiji Mai Runduna ya aike ni gare ki.
“Ya Ubangiji, ƙarfina da kagarata, Mafakata a ranar wahala, A gare ka al'ummai za su zo, Daga ƙurewar duniya, su ce, ‘Kakanninmu ba su gāji kome ba, sai ƙarya, Da abubuwan banza marasa amfani.’
Sa'an nan mala'ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji waɗansu muryoyi masu ƙara a Sama, suna cewa, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Almasihunsa, shi kuma zai yi mulki har abada abadin.”
“Mutane daga kowaɗanne sassa na duniya za su girmama ni. Ko'ina za su ƙona mini halattacciyar hadaya, gama dukansu za su girmama ni,” in ji Ubangiji Mai Runduna.
Ta haka jama'ar Isra'ila za ta ci nasara bisa sauran ƙasar Edom wadda ta ragu, Da bisa dukan al'umman da a dā su nawa ne,” In ji Ubangiji, wanda zai sa al'amarin ya auku.
“Duk da haka yawan mutanen Isra'ila Zai zama kamar yashi a bakin teku, Wanda ba za a iya aunawa ko ƙidayawa ba. Maimakon kuma a ce, ‘Ku ba mutanena ba ne,’ Za a ce, ‘Ku mutanen Allah ne mai rai.’
Ubangiji ya ce mini, “Bawana, ina da aiki mai girma dominka, Ba komo da girman jama'ar Isra'ila da suka ragu kaɗai ba, Amma zan sa ka zama haske ga al'ummai, Domin dukan duniya ta tsira.”
Rana tana zuwa sa'ad da sabon sarki zai fito daga cikin gidan sarautar Dawuda, zai zama alama ga sauran al'umma. Za su tattaru a birnin sarautarsa su girmama shi.
Da ma a yi ta tunawa da sunansa har abada, Da ma shahararsa ta ɗore muddin rana tana haskakawa. Da ma dukan sauran al'umma su yabi sarkin, Dukan jama'a su roƙi Allah yă sa musu albarka, Kamar yadda ya sa wa sarki albarka.
sai ka kasa kunne ga addu'arsa. Ka ji daga Sama, wurin zamanka, ka amsa masa abin da ya roƙe ka, domin dukan mutanen duniya su san sunanka, su kuma yi tsoronka kamar jama'arka, Isra'ilawa, domin kuma su sani wannan Haikali da na gina wurin da za a yi maka sujada ne.
Ubangiji ya ce wa Isra'ila, “Dukiyar Masar da ta Habasha za ta zama taku, Dogayen mutanen Seba kuma za su zama bayinku, Za su bi ku suna a ɗaure da sarƙoƙi. Za su rusuna a gabanku su tuba, su ce, ‘Allah yana tare da ku, shi kaɗai ne Allah.’ ”
Zai shara'anta tsakanin al'umman duniya masu yawa, Zai sulhunta jayayyar da take tsakanin manyan al'ummai, Za su mai da takubansu garemani, Māsunsu kuma su maishe su wuƙaƙen aske itace. Al'umma ba za ta ƙara fita zuwa yaƙi ba, Ba za su ƙara koyon yaƙi ba.