Maganar ke nan da Ubangiji ya faɗa ta bakin annabawan dā, a lokacin akwai mutane da arziki cikin Urushalima da garuruwa kewaye da ita, a lokacin kuma akwai mutane a Negeb da gindin tuddai.
Ba mu kasa kunne ga bayinka annabawa ba, waɗanda kuwa suka yi magana da sunanka ga sarakunanmu, da shugabanninmu, da kakanninmu, da dukan jama'ar ƙasa.