Zakariya 7:7 - Littafi Mai Tsarki7 Maganar ke nan da Ubangiji ya faɗa ta bakin annabawan dā, a lokacin akwai mutane da arziki cikin Urushalima da garuruwa kewaye da ita, a lokacin kuma akwai mutane a Negeb da gindin tuddai. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20207 Ashe, ba kalmomin da Ubangiji ya faɗi ke nan ta bakin annabawan farko ba sa’ad da Urushalima da garuruwan da suke kewaye da ita suke hutawa, suke cikin wadata, akwai kuma mutane a Negeb da yammancin gindin tuddai?’ ” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Za a sayi gonaki da kuɗi, a sa hannu a kan sharuɗa, a hatimce su a gaban shaidu, a ƙasar Biliyaminu da wuraren da suke kewaye da Urushalima, da cikin garuruwan Yahuza, da na garuruwan ƙasar tudu, da a garuruwan kwaruruka, da a garuruwan Negeb, gama zan komar wa mutane da wadatarsu a ƙasarsu, ni Ubangiji na faɗa.”