Suna jin daɗin miƙa hadayu don cin naman, Amma Ubangiji ba ya jin daɗinsu. Ubangiji zai tuna da muguntarsu, Zai hukunta su saboda zunubansu. Za su koma Masar.
Ba za su yi wa Ubangiji hadaya ta sha ba. Ba za su faranta zuciyarsa da sadakoki ba. Abincinsu zai zama irin na masu makoki. Duk wanda ya ci shi zai haramta. Gama abincinsu zai yi musu maganin yunwa ne kawai, Ba za su kai shi Haikalin Ubangiji ba.
Sai suka ci, suka sha, suka yi murna a gaban Ubangiji a wannan rana. Sai suka sake shelar naɗin Sulemanu ɗan Dawuda sarki, a karo na biyu, suka shafa masa man keɓewa domin ya zama mai mulki na Ubangiji, Zadok kuwa shi ne firist.
Amma Ubangiji ya ce masa, “Kada ka kula da kyan tsarinsa, ko tsayinsa, domin ba shi nake so ba, gama yadda Ubangiji yake gani, ba haka mutum yake gani ba. Mutum yakan dubi kyan tsari ne kawai, amma Ubangiji yakan dubi zuciya.”
ku kashe kuɗin a kan duk abin da kuke so, ko sa ne, ko tunkiya, ko ruwan inabi, ko abin sha mai gafi, ko dai duk irin abin da ranku yake so. Nan za ku yi liyafa a gaban Ubangiji Allahnku, ku yi murna tare da iyalan gidanku.
Ba ku kawo mini hadayun ƙonawa na tumaki ba, Ba ni kuke girmamawa da hadayunku ba. Ban nawaita muku da neman hadayu ba, Ko in gajiyar da ku da roƙon turare.
Mutane sukan ce, “Me ya sa muka yi azumi, Ubangiji bai gani ba? Me ya sa muka ƙasƙantar da kanmu, Ubangiji kuwa bai kula ba?” Ubangiji ya ce musu, “Duba, a ranar da kuke azumi, nishaɗin kanku kuke nema, kuna zaluntar dukan ma'aikatanku.
in faɗa wa dukan mutanen ƙasar da firistoci, in ce, “Sa'ad da kuka yi azumi da baƙin ciki a watan biyar da na bakwai dukan shekarun nan saba'in, saboda ni ne kuka yi azumin?
Maganar ke nan da Ubangiji ya faɗa ta bakin annabawan dā, a lokacin akwai mutane da arziki cikin Urushalima da garuruwa kewaye da ita, a lokacin kuma akwai mutane a Negeb da gindin tuddai.