Sai ya ɗauke ni ya tafi da ni zuwa jeji, Ruhu yana iza ni, sai na ga wata mace a kan wata dabba ja wur, duk jikin dabbar sunayen saɓo ne, tana kuma da kawuna bakwai, da ƙaho goma.
Karusar da akawalai suke ja, za ta tafi ƙasar arewa, wadda kuma dawakai kiliyai suke ja, za ta bi su. Wadda kuwa hurde suke ja, za ta tafi ƙasar kudu.”