Zakariya 6:12 - Littafi Mai Tsarki12 Ka kuwa ce masa, ‘Ubangiji Mai Runduna ya ce, mutumin da sunansa Reshe, zai yi girma a inda yake, zai kuma gina Haikalin Ubangiji. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202012 Ka ce masa ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ga mutumin da sunansa ne Reshe, zai kuma ratse daga inda yake yă gina haikalin Ubangiji. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
A watan biyu na shekararsu ta biyu da suka komo wurin Haikalin Allah a Urushalima, sai Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, da Yeshuwa ɗan Yehozadak, da sauran 'yan'uwansu firistoci, da Lawiyawa da dukan waɗanda suka komo Urushalima daga bauta suka fara aikin ginin. Suka sa Lawiyawa 'yan shekara ashirin zuwa gaba su yi shugabancin aikin ginin Haikalin Ubangiji.