1 Da na ɗaga idona sama kuma, sai na ga littafi mai tashi a sama.
1 Na sāke dubawa sai ga naɗaɗɗen littafi mai firiya a gabana!
Sai mala'ikan ya tambaye ni ya ce, “Me ka gani?” Na amsa, “Na ga littafi mai tashi a sama, tsawonsa kamu ashirin ne, fāɗinsa kuma kamu goma.”
Ubangiji ya ce mini, “Ka ɗauki allo babba ka rubuta a kansa da manyan harufa, ‘Kwashe ganima nan da nan, washe da hanzari.’
Ga wani ƙaramin littafi a buɗe a hannunsa. Sai ya tsai da ƙafarsa ta dama a kan teku, ƙafarsa ta hagu kuwa a kan ƙasa,