Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Zakariya 4:9 - Littafi Mai Tsarki

9 “Zarubabel ne ya ɗora harsashin ginin Haikalin nan da hannunsa, shi ne kuma zai gama ginin da hannunsa. Sa'an nan za ka sani Ubangiji Mai Runduna ya aike ni zuwa gare ka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 “Hannuwan Zerubbabel sun kafa harsashin haikalin nan; hannuwansa ne kuma za su gama ginin. Sa’an nan ne za ka san cewa Ubangiji Maɗaukaki ne ya aiko ni zuwa wurinka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Zakariya 4:9
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sheshbazzar kuwa ya zo ya aza harsashin ginin Haikalin Allah wanda yake a Urushalima. Tun daga wannan lokaci, har yanzu ana ta gininsa, har yanzu kuma ba a gama ba.


“Waɗanda yake nesa za su zo su gina Haikalin Ubangiji. Za ku kuwa sani Ubangiji Mai Runduna ya aiko ni wurinku. Wannan zai faru idan kun yi biyayya sosai da muryar Ubangiji Allahnku.”


muna zuba ido ga Yesu, shi da yake shugaban bangaskiyarmu, da kuma mai kammala ta, wanda domin farin cikin da aka sa a gabansa ya daure wa gicciye, bai mai da shi wani abin kunya ba, a yanzu kuma a zaune yake a dama ga kursiyin Allah.


domin dukansu su zama ɗaya, kamar yadda kai, ya Uba, kake cikina, ni kuma nake cikinka, haka su ma su kasance cikinmu, domin duniya ta gaskata, cewa kai ne ka aiko ni.


Gama Allah bai aiko Ɗansa duniya domin yă yanke mata hukunci ba, sai dai domin duniya ta sami ceto ta wurinsa.


Ina dai gaya maka, kai ne Bitrus, a kan dutsen nan ne zan gina ikilisiyata, wadda ikon Hades ba zai rinjaye ta ba.


“A wannan rana al'umman duniya da yawa za su haɗa kai da Ubangiji, za su kuwa zama jama'ata, ni kuma zan zauna a tsakiyarki. Za ki sani Ubangiji Mai Runduna ya aike ni gare ki.


“Yanzu fa, sai ku matso kusa da ni, Ku ji abin da nake faɗa. Tun da farko na yi magana da ku a fili, A koyaushe nakan cika maganata.” (Yanzu Ubangiji Allah ya ba ni iko, ya kuwa aike ni.)


Yanzu ku tuna a ran nan, wato rana ta ashirin da huɗu ga watan tara, tun daga ranar da aka aza harsashin ginin Haikalin Ubangiji.


Saboda haka shi Ubangiji zai koma ya ji juyayin Urushalima. Za a gina Haikalinsa a cikinta, zai kuma auna Urushalima da ma'auni.”


Bari dukan 'yan adam su yi tsit a gaban Ubangiji, gama ya taso daga wurin zamansa mai tsarki.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ