‘Mene ne kai, ya babban dutse? Za ka zama fili a gaban Zarubabel, zai kuwa kwaso duwatsun da suke ƙwanƙoli da sowa, yana cewa alheri, alheri ne ya kawo haka.’ ”
“Zarubabel ne ya ɗora harsashin ginin Haikalin nan da hannunsa, shi ne kuma zai gama ginin da hannunsa. Sa'an nan za ka sani Ubangiji Mai Runduna ya aike ni zuwa gare ka.
“Waɗanda yake nesa za su zo su gina Haikalin Ubangiji. Za ku kuwa sani Ubangiji Mai Runduna ya aiko ni wurinku. Wannan zai faru idan kun yi biyayya sosai da muryar Ubangiji Allahnku.”