Zakariya 4:6 - Littafi Mai Tsarki6 Sa'an nan ya ce, “Wannan ita ce maganar Ubangiji zuwa ga Zarubabel cewa, ‘Ba da ƙarfi, ko iko ba, amma da Ruhuna,’ in ji Ubangiji Mai Runduna. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20206 Sai ya ce mini, “Wannan ce maganar Ubangiji ga Zerubbabel. ‘Ba ta wurin ƙarfi ba, ko ta wurin iko, sai dai ta wurin Ruhuna,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Asa kuwa ya yi kuka ga Ubangiji Allahnsa, ya ce, “Ya Ubangiji, ba wani mai taimako kamarka, wanda zai yi taimako sa'ad da mai ƙarfi zai kara da marar ƙarfi, ka taimake mu, ya Ubangiji Allahnmu, gama a gare ka muke dogara, da sunanka kuma muka zo don mu yi yaƙi da wannan babbar runduna. Ya Ubangiji, kai ne Allahnmu, kada ka bar mutum ya rinjayi jama'arka.”