Dukanmu muka cika da zunubi har ayyukanmu mafi kyau ƙazamai ne duka. Saboda zunubanmu, muka zama kamar busassun ganyaye waɗanda iska take faucewa ta tafi da su.
Ya Ubangiji Allah na Isra'ila, kai mai adalci ne, gama ka bar mana ringin da ya tsira kamar yadda yake a yau. Ga mu nan gabanka da zunubinmu, gama ba wanda zai iya tsayawa a gabanka saboda wannan.”
Ya Allahna, ka karkato kunnenka ka ji, ka buɗe idanunka ka ga yadda mu da birnin da ake kira da sunanka muka lalace. Ba cewa muna da wani adalci na kanmu shi ya sa muka kawo roƙe-roƙenmu ba, amma saboda yawan jinƙanka.
kuna ceton waɗansu kuna fizgo su daga wuta. Waɗansu kuma ku ji tausayinsu, amma tare da tsoro kuna ƙyamar ko da tufafin da halinsu na mutuntaka ya ƙazantar.
Sai Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, da Yeshuwa ɗan Yehozodak, suka tashi suka sāke kama aikin gina Haikalin Allah wanda yake a Urushalima. Annabawan Allah suna tare da su, suna taimakonsu.
Ka amince da waɗanda suke murna su aikata abin da yake daidai, su waɗanda suka tuna da yadda kake so su yi zamansu. Ka yi fushi da mu, amma muka ci gaba da yin zunubi, har da fushin da ka yi ƙwarai, muka ci gaba da aikata abin da ba daidai ba, tun daga zamanan dā.