Ku gudu daga cikin Babila, Bari kowa ya ceci ransa, Kada a hallaka ku tare da ita, Gama a wannan lokaci Ubangiji zai sāka mata, Zai sāka mata bisa ga alhakinta.
Ku fita, ku bar Babila Ku dukanku da kuke ɗauke da keɓaɓɓen kayan Ubangiji! Kada ku taɓa abin da aka hana, Ku kiyaye kanku da tsarki, Ku fita ku bar birnin.
Sa'ad da suka fitar da shi, suka ce, “Ka gudu domin ranka, kada ka waiwaya baya, ko ka tsaya ko'ina cikin kwari, gudu zuwa tuddai domin kada a hallaka ka.”
Ki yi makyarkyata, ki yi nishi, ke Sihiyona, Kamar mace mai naƙuda, Gama yanzu za ki fita daga cikin birni, Ki zauna a karkara, Za ki tafi Babila, daga can za a cece ki. Daga can Ubangiji zai cece ki daga hannun maƙiyanki.
Ki kakkaɓe kanki, ya Urushalima! Ki tashi daga cikin ƙura, Ki hau gadon sarautarki. Ki ɓaɓɓale sarƙoƙin da suke ɗaure da ke, Ke kamammiyar jama'ar Sihiyona!
Sai ya ce wa jama'ar, “Ina roƙonku, ku ƙaurace wa alfarwan waɗannan mugayen mutane, kada ku taɓa kowane abu da yake nasu, domin kada a shafe ku saboda zunubansu.”
Ubangiji ya ce, “Babila, ki sauko daga kan gadon sarautarki, Ki zauna a ƙasa cikin ƙura. Dā ke budurwa ce, birnin da ba a yi nasara da shi ba! Amma ba sauran taushi da kuma rashin ƙarfi! Ke baiwa ce yanzu!