Zakariya 2:11 - Littafi Mai Tsarki11 “A wannan rana al'umman duniya da yawa za su haɗa kai da Ubangiji, za su kuwa zama jama'ata, ni kuma zan zauna a tsakiyarki. Za ki sani Ubangiji Mai Runduna ya aike ni gare ki. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202011 “Ƙasashe da yawa za su haɗa kai da Ubangiji a ranan nan, za su kuma zama mutanena. Zan zauna a cikinku, za ku kuma san cewa Ubangiji Maɗaukaki ne ya aiko ni gare ku. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
su kuwa sani ni ne wanda yake hukunta musu. “Amma zan bar waɗansu, in aika da su ga al'ummai da manisantan ƙasashe inda ba a ji labarin sunan da na yi ba, ba a kuwa ga girmana da ikona ba, wato zuwa Tarshish, da Libiya, da Lidiya, duk da gwanayen maharbanta, Rosh da Tubal, da kuma Helas. Za su ba da labarin girmana ga waɗannan al'ummai.