Zakariya 2:10 - Littafi Mai Tsarki10 “Ki raira waƙa, ki yi farin ciki, ya Sihiyona, gama ina zuwa, in zauna a tsakiyarki! Ni Ubangiji na faɗa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202010 “Ki yi sowa ki yi murna, ya ke Diyar Sihiyona. Gama ina zuwa, zan zauna a cikinki,” in ji Ubangiji. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
za a sāke jin muryar murna da ta farin ciki, da muryar ango da ta amarya, da muryoyin mawaƙa, sa'ad da suke kawo hadayun godiya a cikin Haikalin Ubangiji, suna cewa, “ ‘Ku yi godiya ga Ubangiji Mai Runduna, Gama Ubangiji nagari ne, Gama madawwamiyar ƙaunarsa tabbatacciya ce.’ “Gama zan mayar da arzikin ƙasar kamar yadda yake a dā, ni Ubangiji na faɗa.”