Sa'ad da ya kai ni can sai ga wani mutum, kamanninsa sai ka ce tagulla, yana riƙe da igiyar rama da wani irin ƙara na awo a hannunsa, yana tsaye a bakin ƙofa.
Sai kuma ya auna kamu dubu, ya sa ni in haye ruwan. Zurfin ruwan kuwa ya kama ni gwiwa. Sai ya sāke auna kamu dubu, ya sa in haye ruwan, sai zurfin ruwan ya kai ga kama ni gindi.
Abin da na gani Haikali ne. Akwai katanga kewaye da filin Haikalin. Tsawon karan awon kuma da yake a hannun mutumin kamu shida ne. Sai ya auna faɗin katangar ya sami kamu shida, tsayinta kuma kamu shida.
“Bayan wannan kuma a wahayi na dare na ga dabba ta huɗu mai ƙarfi ƙwarai, mai bantsoro da banrazana. Tana da haƙoran ƙarfe, zaga-zaga. Ta cinye, ta ragargaza, sa'an nan ta tattake sauran da ƙafafunta. Dabam take da sauran dabbobin da suka riga ta. Tana kuma da ƙaho goma.