Ya ce masa, “Ka yi gudu, ka faɗa wa saurayin can, cewa za a zauna a Urushalima kamar a ƙauyuka marasa garu, saboda yawan mutane da dabbobi da suke cikinta.
“Sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji Allahnku, Wanda yake zaune a Sihiyona, tuduna tsattsarka. Urushalima kuma za ta tsarkaka, Sojojin abokan gāba ba za su ƙara ratsawa ta cikinta ba.
Dukan filin kwarin gawawwaki da toka, da dukan filaye har zuwa rafin Kidron zuwa kan kusurwar Ƙofar Doki wajen gabas, za su zama mai tsarki ga Ubangiji. Ba za a ƙara tumɓuke shi ko a rushe shi ba har abada.”
Ba za a ƙara jin hayaniyar tashin hankali ba, Ba za a ƙara aukar wa ƙasar da ɓarna ba. Zan kiyaye ki, in kāre ki kamar garu, Za ki yi yabona domin na cece ki.
Ubangiji kuwa ya ji wa'adin Isra'ilawa, ya kuwa ba su Kan'aniyawa, suka hallaka su da biranensu ƙaƙaf. Don haka aka sa wa wurin suna Horma, wato hallakarwa.
Ga shi, zan tattaro su daga dukan ƙasashe inda na kora su, da fushina, da hasalata, da haushina. Zan komo da su a wannan wuri, zan sa su su zauna lafiya.
Ya jama'ar Yahuza da jama'ar Isra'ila, kamar yadda kuka zama abin la'antarwa a cikin al'ummai, haka kuma zan cece ku, ku zama masu albarka, kada ku ji tsoro, amma ku himmantu.
“A ranan nan zan sa iyalan Yahuza su zama kamar wuta a kurmi, ko kuwa a gonar da hatsi ya nuna. Za su halaka dukan al'umman da suke kewaye da su. Amma mutanen Urushalima za su yi zamansu lami lafiya.