Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Zakariya 13:2 - Littafi Mai Tsarki

2 A wannan rana fa, ni Ubangiji Mai Runduna, zan shafe sunayen gumaka daga ƙasar, har da ba za a ƙara tunawa da su ba. Zan kuma kawar da annabawa da mugayen aljannu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 “A ranan nan, zan kawar da sunayen gumaka daga ƙasar, ba kuwa za a ƙara tunawa da su ba,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Zan kawar da annabawa da kuma ruhu marar tsabta daga ƙasar.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Zakariya 13:2
40 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ubangiji ya ce masa, ‘Ta wace hanya?’ Sai ruhun ya ce, ‘Zan tafi in zama ruhun ƙarya a bakin dukan annabawansa.’ Sai Ubangiji ya ce, ‘Ba shakka za ka yaudare shi, za ka yi nasara, sai ka tafi.’ ”


Zan kawar da sunayen Ba'al daga bakinta. Ba za a ƙara kiransu da sunayensu ba.


Ku kula da dukan abin da na faɗa muku. Kada a ji bakinku na roƙon kome ga waɗansu alloli.”


Zan yayyafa muku tsabtataccen ruwa, za ku kuwa tsarkaka daga dukan ƙazantarku, da kuma daga dukan gumakanku.


Ubangiji Allah ya ce, “Zan hallakar da gumaka Da siffofi a Memfis. Ba za a ƙara samun hakimi a ƙasar Masar ba, Saboda haka zan aukar da tsoro a ƙasar Masar.


Sai aka kama dabbar, da kuma annabin nan na ƙarya tare da ita, wanda ya yi al'ajabai a gabanta, waɗanda da su ne ya yaudari waɗanda suka yarda a yi musu alamar dabbar nan, da kuma waɗanda suka yi wa siffarta sujada. Waɗannan biyu kuwa aka jefa su da ransu a cikin tafkin wuta da ƙibiritu.


Ni kuwa in da ikon Allah nake fitar da aljannu, ashe, Mulkin Allah ya zo muku ke nan.


“Baƙin aljan in ya rabu da mutum, sai ya bi ta wurare marasa ruwa neman hutu, amma ba ya samu.


Ubangiji zai tsananta musu, Zai kawo wa dukan gumakan da yake a duniya yunwa. Kowane mutum a duniya zai yi masa sujada a inda yake, Har da ƙasar sauran al'umma.


“Idan mutum ya tashi yana iskanci, yana faɗar ƙarya, ya ce, ‘Zan yi muku wa'azi game da ruwan inabi da abin sa maye,’ To, shi ne zai zama mai wa'azin mutanen nan!


Ba za su ƙara ƙazantar da kansu da gumaka da abubuwan banƙyama da kowane irin laifi ba. Zan komo da su daga riddar da suka yi, in tsarkake su. Za su zama jama'ata, ni kuma zan zama Allahnsu.


“ ‘Idan aka ruɗi annabin har ya yi magana, ni Ubangiji, ni ne na rinjaye shi, zan miƙa hannuna gāba da shi, zan hallaka shi daga cikin mutanena, Isra'ila.


Domin haka ba za ku ƙara ganin wahayin ƙarya ba, ko ku yi dūba. Zan ceci mutanena daga hannunku. Sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji.”


Gama sun yi wauta a Isra'ila, sun yi zina da matan maƙwabtansu, sun yi ƙarya da sunana, ni kuwa ban umarce su ba. Ni na sani, ni ne kuma shaida, ni Ubangiji na faɗa.”


Sa'ad da wannan rana ta yi za su zubar da gumakan da suka yi na zinariya da azurfa, za su bar wa ɓeraye da jemagu.


Waɗanda suke hanzari zuwa ga gumaka, Za su jawo wa kansu wahala. Ba zan yi tarayya da su da hadayarsu ba. Ba zan yi sujada ga gumakansu ba.


domin kada ku yi cuɗanya da sauran al'umman da take zaune tare da ku, kada ku ambaci sunayen gumakansu, ko ku rantse da su, ko ku bauta musu, ko ku sunkuya musu.


Sai ku rurrushe bagadansu, ku ragargaje al'amudansu, ku ƙone ginshiƙansu na tsafi, ku kuma sassare siffofin gumakansu, ku shafe sunayensu daga wuraren nan.


Idan kuwa naman jeji ne ya kashe ta, zai nuna gawar don shida. Ba zai yi ramuwar abin da naman jeji ya kashe ba.


Sai ya yi kira da murya mai ƙarfi, ya ce, “Ta fāɗi! Babila mai girma ta fāɗi! Ta zama mazaunin aljannu, Matattarar kowane baƙin aljani, Da kowane irin ƙazamin tsuntsu, abin ƙyama.


“Ku kula da annabawan ƙarya, waɗanda sukan zo muku da siffar tumaki, amma a zuci kyarketai ne masu ƙāwa.


Ya mutanen Ifraimu, me zan yi da gumaka? Ni ne wanda yake amsa muku, mai lura da ku kuma. Ni kamar itacen fir ne mai ganyaye kore shar. Daga gare ni, kuke samun 'ya'ya.”


A duk inda kuke zaune, biranenku za su zama kango, wuraren tsafinku da bagadanku za su lalace, gumakanku da bagadanku na ƙona turare za a farfashe su. Za a shafe dukan abin da kuka yi.


“Wahayin ƙarya da dūbā na kiran kasuwa za su ƙare a Isra'ila.


Zan tsarkake ku daga dukan ƙazantarku. Zan kuma sa hatsi ya yi yalwa, ba zan bar yunwa ta same ku ba.


Amma duk wani annabin da ya yi izgili yana magana da sunana, ni kuwa ban umarce shi ba, ko kuwa yana magana da sunan gumaka, wannan annabi zai mutu.’


Ya ce mini, “Ɗan mutum, wannan wuri shi ne kursiyin sarautata da kilisaina, inda zan zauna tsakiyar mutanen Isra'ila har abada. Mutanen Isra'ila da sarakunansu ba za su ƙara ɓata sunana mai tsarki ta wurin bauta wa gumaka da gina siffofin sarakunansu da suka mutu ba,


Zan ɗaura auren da yake cikin adalci, Da bisa kan ka'ida, da ƙauna.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ