Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Zakariya 12:11 - Littafi Mai Tsarki

11 A ran nan za a yi babban makoki a Urushalima kamar mutane suka yi wa Hadadrimmon a filin Magiddo.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 A ranan nan kuka a Urushalima zai yi yawa kamar kukan Hadad Rimmon a filin Megiddo.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Zakariya 12:11
7 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Barorinsa kuwa suka ɗauke shi daga cikin karusa, suka sa shi a karusa ta biyu, suka kawo shi Urushalima, sai ya rasu. Aka binne shi a hurumin kakanninsa. Yahuza da Urushalima fa suka yi makoki domin Yosiya.


A zamaninsa Fir'auna-neko, Sarkin Masar, ya tafi ya tasar wa Sarkin Assuriya da yaƙi a Kogin Yufiretis. Sarki Yosiya kuwa ya yi ƙoƙari ya hana shi wucewa, sa'ad da Fir'auna-neko ya gan shi, sai ya kashe shi a filin yaƙi a Magiddo.


A sa'an nan ne alamar Ɗan Mutum za ta bayyana a sararin sama, duk kabilan duniya kuma za su yi kuka, za su ga Ɗan Mutum yana zuwa kan gajimare, da iko da ɗaukaka mai yawa.


Ga shi, zai zo a cikin gajimare, kowa zai gan shi, har da waɗanda suka soke shi, duk kabilan duniya kuma za su yi kuka a kansa. Wannan haka yake. Amin.


Sai suka tattara su a wurin da ake kira Armageddon da Yahudanci.


Kowane iyali a ƙasar za su yi makokinsu a keɓe, iyalin gidan Dawuda kuma za su yi nasu a keɓe, matansu za su yi nasu a keɓe. Iyalin gidan Natan su ma za su yi nasu makoki a keɓe, matansu kuma a keɓe.


Duk da haka Yosiya bai yarda ya koma ba, sai ya ɓad da kama don ya yi yaƙi da shi. Bai yarda da magana wadda Allah ya faɗa wa Neko ba, sai suka kama yaƙi a filin Magiddo.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ