Annabawanki sun gano miki wahayan ƙarya, Ba su tone asirin muguntarki, Har da za a komo da ke daga bauta ba. Amma suka yi miki annabcin ƙarya na banza.
“Taka ta ƙare, kai makiyayi marar amfani, Wanda yakan bar tumakin! Da ma takobi ya sari dantsensa da idonsa na dama! Da ma hannunsa ya shanye sarai, Idonsa na dama kuma ya makance!”