Zakariya 11:12 - Littafi Mai Tsarki12 Sai na ce musu, “Idan kun ga daidai ne sai ku biya ni hakkina, idan kuwa ba haka ba ne, to, ku riƙe abinku!” Sai suka biya ni tsabar azurfa talatin, ladana. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202012 Na faɗa musu cewa, “In kun ga ya fi kyau, ku biya ni; in kuwa ba haka ba, ku riƙe.” Saboda haka suka biya ni azurfa talatin. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Zan zo wurinku domin in yi shari'a. Nan da nan zan tabbatar da laifin masu yin sihiri, da na mazinata, da na masu shaidar zur, da na masu zaluntar ma'aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu, da marayu, da baƙi, da waɗanda ba su ganin girmana.”