Ɓarnar da aka yi wa Lebanon za ta komo kanka, Ka kashe dabbobinta, yanzu dabbobi za su tsorata ka, Saboda jinin mutanen da ka zubar, Da wulakancin da ka yi wa duniya, Da birane, da mazauna a cikinsu.
Saboda ka washe al'umman duniya da yawa, Sauran mutanen duniya duka za su washe ka, Saboda jinin mutane, da wulakancin da ka yi wa duniya, Da birane, da mazauna a cikinsu.
Ka yi kuka, kai itacen kasharina, Gama itacen al'ul ya riga ya fāɗi, Itatuwa masu daraja sun lalace, Ku yi kuka, ku itatuwan oak na Bashan, Saboda an sassare itatuwan babban kurmi.
“A ranan nan zan sa iyalan Yahuza su zama kamar wuta a kurmi, ko kuwa a gonar da hatsi ya nuna. Za su halaka dukan al'umman da suke kewaye da su. Amma mutanen Urushalima za su yi zamansu lami lafiya.