Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Zakariya 10:6 - Littafi Mai Tsarki

6 “Zan sa jama'ar Yahuza ta yi ƙarfi, Zan ceci jama'ar Yusufu. Zan dawo da su domin ina jin tausayinsu. Za su zama kamar waɗanda ban taɓa ƙyale su ba, Gama ni Ubangiji Allahnsu ne, Zan amsa musu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 “Zan ƙarfafa gidan Yahuda in kuma ceci gidan Yusuf. Zan maido da su domin ina jin tausayinsu. Za su zama kamar ban taɓa ƙinsu ba, gama ni ne Ubangiji Allahnsu zan kuma amsa musu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Zakariya 10:6
39 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sulusi ɗayan da ya ragu kuwa zan tura cikin wuta, Zan tace su da wuta kamar yadda akan tace azurfa, Zan gwada su kamar yadda akan gwada zinariya. Za su kira gare ni, Zan kuwa amsa musu, Zan ce, ‘Su jama'ata ne,’ Su kuma za su ce, ‘Ubangiji shi ne Allahnmu.’ ”


Zan ƙarfafa su, Za su yi tafiya da sunansa, Ni Ubangiji na faɗa.”


A waɗannan kwanaki mutanen Yahuza za su haɗu da mutanen Isra'ila. Tare za su zo daga ƙasar arewa zuwa cikin ƙasar da na ba kakanninku gādo.”


Amma yanzu ba zan yi da sauran jama'an nan kamar yadda na yi a kwanakin dā ba, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.


Mutanen Yahuza da mutanen Isra'ila za su haɗu su zama ɗaya, Za su zaɓa wa kansu shugaba ɗaya. Za su shugabanci ƙasar Gama ranar Yezreyel babba ce.”


Ubangiji Allah ya ce, “Ga abin da zan sa mutanen Isra'ila su roƙe ni, in yi musu. Za su roƙe ni in yawaita su kamar garken tumaki.


Kada ka ji tsoro, ina tare da kai, Ni ne Allahnka, kada ka bar kome ya firgita ka. Zan sa ka yi ƙarfi, in kuma taimake ka, Zan kiyaye ka, in cece ka.


Al'umman duniya za su gani, Su kuwa ji kunyar ƙarfinsu duka. Za su sa hannuwansu a baka, Kunnuwansu za su kurmance.


Ringin Yakubu kuma zai zamar wa al'umman duniya, Kamar yadda zaki yake a tsakanin namomin jeji, Kamar kuma yadda zaki yake a tsakanin garkunan tumaki, Wanda, sa'ad da ya ratsa, yakan tattaka, Ya yi kacakaca da su, Ba wanda zai cece su.


“Ya Sihiyona, ki tashi, ki tattaka! Gama zan mai da ƙahonki ƙarfe, kofatanki kuwa tagulla, Za ki ragargaje al'ummai da yawa.” Za ki ba Ubangijin dukan duniya dukiyarsu da suka tara ta hanyar zamba, Wadatarsu kuma ga Ubangijin dukan duniya.


Zan dasa ta a ƙasa domin kaina. Zan kuma yi wa ‘Ba-jinƙai,’ jinƙai, In kuma ce wa ‘Ba-mutanena ba,’ ‘Mutanena!’ Su ma za su ce, ‘Kai ne Allahna!’ ”


Ubangiji zai sāke yi wa jama'arsa Isra'ila jinƙai, ya zaɓe su su zama nasa. Zai sāke sa su zauna a ƙasarsu, baƙi ma za su zo su zauna tare da su.


“Saboda haka, ni Ubangiji Allah, na ce yanzu zan komo da zuriyar Yakubu daga bauta in nuna mata jinƙai. Zan yi kishi domin sunana mai tsarki.


“Ɗan mutum, ka ɗauki sanda, ka rubuta a kansa, ‘Domin Yahuza da magoyan bayansa.’ Ka kuma ɗauki wani sanda, ka rubuta a kansa, ‘Domin Yusufu, sandan Ifraimu, da dukan mutanen Isra'ila, magoyan bayansa.’


Zan sa mutum da dabba su yawaita a cikinku, su kuma ba da amfani. Zan sa a zauna a cikinku kamar dā, sa'an nan zan nuna muku alheri fiye da dā. Daga nan za ku sani, ni ne Ubangiji.


Ubangiji ya ce, “Ga shi, kwanaki suna zuwa da zan yi sabon alkawari da mutanen Isra'ila da na Yahuza.


Ashe, Ifraimu ba ƙaunataccen ɗana ba ne? Ashe, shi ba ɗan gaban goshina ba ne? A duk lokacin da na ambace shi a kan muguntarsa Nakan tuna da shi da ƙauna. Saboda na ƙwallafa zuciyata a kansa, Hakika zan yi masa jinƙai, ni Ubangiji na faɗa.


Ubangiji ya ce, “Lokaci yana zuwa da zan zama Allah na dukan iyalan Isra'ila, za su kuwa zama jama'ata.”


Ubangiji ya ce, “Ga shi, zan komar wa alfarwar Yakubu arzikinta, Zan kuma nuna wa wuraren zamansa jinƙai, Za a sāke gina birnin a kufansa, Fādar kuma za ta kasance a inda take a dā.


A zamaninsa za a ceci Yahuza, Isra'ila kuwa za ta zauna lafiya. Sunan da za a kira shi da shi ke nan, ‘Ubangiji Adalcinmu.’


Ƙarfina zai kasance tare da shi, Ikona kuma zai ƙarfafa shi.


Ubangiji ya ce, “A waccan rana zan tattara guragu, Da waɗanda aka kora, Da waɗanda na wahalshe su.


Jama'ar Yakubu za ta zama kamar wuta, Jama'ar Yusufu kuwa kamar harshen wuta, Jama'ar Isuwa za ta zama kamar tattaka. Za su ƙone ta, su ci ta, ba wanda zai tsira. Ni Ubangiji na faɗa.”


Amma zan yi wa mutanen Yahuza jinƙai. Ni kaina zan cece su ba da baka ba, ba kuwa da takobi, ko da yaƙi, ka da dawakai, ko da sojojin dawakai ba.”


Ubangiji zai ɗaga tuta, alama ce ta nuna wa sauran al'umma, ya sāke tattara jama'ar Isra'ila da ta Yahuza waɗanda aka warwatsa, ya sāke komo da su daga kusurwoyi huɗu na duniya.


Kada ki ji tsoro, ba za a ƙara kunyatar da ke ba, Ba kuwa za a ƙasƙantar da ke ba. Za ki manta da rashin amincinki irin na matar ƙuruciya, Za ki manta da matsanancin kaɗaicinki, Mai kama da na gwauruwa.


Na juya, na rabu da ke da fushi na ɗan lokaci, Amma zan nuna miki ƙaunata har abada.” Haka Ubangiji mai fansarki ya faɗa, shi wanda ya cece ki.


Saboda haka shi Ubangiji zai koma ya ji juyayin Urushalima. Za a gina Haikalinsa a cikinta, zai kuma auna Urushalima da ma'auni.”


A wannan rana Ubangiji Allahnsu zai cece su, Gama su jama'arsa ne, garkensa kuma, Kamar yadda lu'ulu'u yake haske a kambi, Haka za su yi haske a ƙasarsa.


'Ya'yansu za su zama kamar dā, Jama'arsu kuma za su kahu a gabana, Zan hukunta dukan waɗanda suka zalunce su.


Duk wanda yake da hikima, bari ya fahimci abubuwan nan. Duk wanda yake da ganewa, bari ya san abubuwan nan, Gama hanyoyin Ubangiji masu gaskiya ne, Masu adalci kuwa za su yi tafiya a cikinsu, Amma masu zunubi za su yi tuntuɓe a kansu.


Domin haka zai yashe su, Sai lokacin da wadda take naƙuda ta haihu. Sa'an nan sauran 'yan'uwansa Za su komo wurin mutanen Isra'ila.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ