Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Zakariya 1:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Da dare, na ga mutum yana kan aharashin doki, yana tsaye a cikin itatuwan ci-zaƙi, a kwari. A bayansa kuma ga wani aharashin doki, da bidi, da kili.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Da dare, na ga wahayi, a gabana kuwa ga mutum a kan jan doki! Yana tsaye a cikin itatuwa masu furanni, a bayansa a cikin itatuwan ci-zaƙi, a bayansa kuwa akwai dawakai masu ruwan ja, ruwan ƙasa-ƙasa da kuma ruwan fari.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Zakariya 1:8
26 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai wani jan doki ya fito, aka kuma ba mahayinsa izini yă ɗauke salama daga duniya, don mutane su kashe juna, aka kuma ba shi babban takobi.


“Sai ka rubuta wa mala'ikan ikkilisiyar da take a Afisa haka, ‘Ga maganar wadda take riƙe da taurarin nan bakwai a hannunsa na dama, wadda kuma take tafiya a tsakiyar fitilun nan bakwai na zinariya.


“Ka farka, ya kai takobi, ka fāɗa wa makiyayina, Ka fāɗa wa mutumin da yake kusa da ni, Ka sari makiyayin domin tumakin su watse. Zan bugi ƙanana da hannuna, Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.


Itacen fir zai tsiro a wurin da sarƙaƙƙiya take yanzu, Itacen ci-zaƙi zai tsiro a maimakon ƙayayuwa. Wannan zai zama alamar da za ta kasance har abada, Matuni ne na abin da ni, Ubangiji, na yi.”


Zan sa itatuwan al'ul su tsiro a hamada, Da itacen ƙirya, da itacen ci-zaki, da zaitun. Ƙeƙasasshiyar ƙasa za ta zama kurmi, Jejin itatuwan fir.


“A cikin wahayi na dare, na ga wani kamar Ɗan Mutum. Yana zuwa cikin gizagizai, Ya zo wurin wanda yake Tun Fil Azal, Aka kai shi gabansa.


Daniyel ya ce, “A wahayi da dare na ga iskar samaniya daga kusurwa huɗu tana gurɓata babbar teku.


Sai aka bayyana wa Daniyel asirin ta cikin wahayi da dare. Daga nan Daniyel ya yabi Allah na Sama.


Gama haka wanda yake can Sama, Maɗaukaki, wanda ake kira Mai Tsarki ya ce, “Ina zaune a can Sama a tsattsarkan wuri, tare kuma da wanda yake da halin tuba mai tawali'u, don in farfaɗo da ruhun masu tawali'u, in kuma farfaɗo da zukatan masu tuba.


Kamar wani irin mafarki mai razanarwa yake, Wanda ya hana ni jin daɗin barcina.


Ubangiji kuwa ya bayyana ga Sulemanu cikin mafarki a Gibeyon da dare, ya ce masa, “Ka roƙi abin da kake so in ba ka.”


Lokacin da Joshuwa yake daura da Yariko, ya ta da idanunsa ya duba, sai ya ga mutum a tsaye a gabansa da takobinsa a zare a hannunsa. Joshuwa ya tafi wurinsa, ya ce masa, “Kana wajenmu ne, ko kuwa kana wajen abokan gābanmu?”


Amma Allah ya zo wurin Abimelek cikin mafarki da dad dare ya ce masa, “Mutuwa za ka yi saboda matar da ka ɗauko, gama ita matar wani ce.”


Ƙaunataccena ya tafi lambunsa inda fangulan furanninsa suke. Yana kiwon garkensa a lambun, yana tattara furannin bi-rana.


Ƙaunataccena nawa ne, ni ma tasa ce, Yana kiwon garkensa a cikin furannin bi-rana,


Da na duba, ga farin doki, mahayinsa kuma yana da baka, aka ba shi kambi, ya kuwa fita yana mai nasara, domin ya ƙara cin nasara.


Saboda haka sai suka yi shela a garuruwansu duka da a Urushalima cewa, “Ku fita zuwa tuddai ku kawo rassan zaitun, da na kadanya, da na dargaza, da na dabino, da sauran rassan itatuwa masu gazari, domin a yi bukkoki kamar yadda aka rubuta.”


A rana ta ashirin da huɗu ga watan goma sha ɗaya, wato watan Shebat, a shekara ta biyu ta sarautar Dariyus, Ubangiji ya kuma yi magana da annabi Zakariya, ɗan Berekiya, ɗan Iddo.


Sai mutumin da yake tsaye a cikin itatuwan ci-zaƙin ya amsa ya ce, “Waɗannan su ne Ubangiji ya aike su su yi tsaron duniya, suna kai da kawowa.”


Sai suka ce wa mala'ikan Ubangiji wanda yake tsaye a cikin itatuwan ci-zaƙin, “Mun yi ta kai da kawowa a duniya, sai muka ga duniya duka tana zaman lafiya.”


Sai Allah ya yi magana cikin wahayin dare, ya ce, “Yakubu.” Ya amsa ya ce, “Na'am.”


Ya ce, “Ku ji abin da zan faɗa! Idan akwai annabawa a cikinku, nakan bayyana gare su cikin wahayi, in kuma yi magana da su ta cikin mafarki.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ