Zakariya 1:21 - Littafi Mai Tsarki21 Sai na ce, “Me waɗannan suke zuwa su yi?” Sai ya ce, “Waɗannan su ne ƙahonin da suka warwatsa Yahuza don kada mutum ya ɗaga kansa. Waɗannan kuwa sun zo don su tsorata su, su karya ƙahonin al'umman duniya waɗanda suka ɗaga ƙahoninsu gāba da ƙasar Yahuza don su warwatsa ta.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202021 Na yi tambaya na ce, “Mene ne waɗannan suke zuwa yi?” Ya amsa ya ce, “Waɗannan ne ƙahonin da suka watsar da Yahuda har ba wanda yake iya ɗaga kansa, amma maƙeran sun zo don su tsorata su su kuma saukar da ƙahonin ƙasashen nan waɗanda suka ɗaga ƙahoninsu gāba da ƙasar Yahuda don su warwatsa ta.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |