Saboda haka ka bar abokan gābansu su ci su, mallake su. A wahalarsu sun yi kira gare ka domin taimako, Ka kuwa amsa musu daga Sama. Ta wurin jinƙanka mai yawa ka aiko musu da shugabanni, Waɗanda suka kuɓutar da su daga maƙiyansu.
Ubangiji kuwa ya aika musu da Yerubba'al, wato Gidiyon, da Barak, da Yefta, da Samson, suka cece ku daga hannun abokan gābanku ta kowace fuska. Sa'an nan kuka yi zamanku lafiya.
“Sa'an nan suka ci gaba da tafiya ta cikin hamada. Suka zaga ƙasar Edom da ta Mowab. Da suka kai gabashin ƙasar Mowab, sai suka yi zango a bakin Kogin Arnon, amma ba su haye kogin ba, gama shi ne iyakar ƙasar Mowab.
Maƙeri yakan ɗauki guntun ƙarfe ya sa shi a wuta ya yi aiki. Da hannunsa mai ƙarfi yana ɗaukar guduma yana bugun ƙarfen, yana mai da shi siffa. Yakan ji yunwa, da ƙishi, yakan kuma ji gajiya.