A cikin annabawa wane ne kakanninku ba su tsananta wa ba? Sun kuma kashe waɗanda suka yi faɗi a kan zuwan Mai Adalcin nan, wanda a yanzu kuka zama maciya amanarsa, da kuma makasansa,
Bayan wannan dukan abubuwan nan suka same mu saboda mugayen ayyukanmu da zunubanmu masu yawa. Ya Allahnmu, ga shi ma, ka hukunta mu kaɗan bisa ga yawan zunubanmu, ka kuma bar mana wannan ringi.
da yake zuciyarka mai tuba ce, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gabana sa'ad da ka ji yadda na yi magana gāba da wannan wuri, da kuma mazaunansa, cewa zai zama kufai da la'ana, kai kuwa ka keta tufafinka, ka yi kuka a gabana, hakika na ji kukanka.
Amma sa'ad da suka shiga cikinta suka mallake ta, ba su yi biyayya da muryarka ba, ba su kiyaye dokokinka ba, ba su aikata dukan abin da ka umarce su ba, saboda haka ka sa wannan masifa ta auko musu.
Suka taurare zuciyarsu kamar dutse don kada su ji dokoki da maganar da ni Ubangiji Mai Runduna na aiko ta wurin Ruhuna zuwa ga annabawa na dā. Domin haka ni Ubangiji Mai Runduna na aukar musu da hasala mai zafi.
“Ni Ubangiji Mai Runduna, na ce, kamar yadda na ƙudura in aukar muku da masifa, ban kuwa fasa ba, lokacin da kakanninku suka tsokane ni, suka sa na yi fushi.