Lokacin da Joshuwa yake daura da Yariko, ya ta da idanunsa ya duba, sai ya ga mutum a tsaye a gabansa da takobinsa a zare a hannunsa. Joshuwa ya tafi wurinsa, ya ce masa, “Kana wajenmu ne, ko kuwa kana wajen abokan gābanmu?”
A zamanin Feka Sarkin Isra'ila, sai Tiglat-filesar mai mulkin Assuriya, ya zo ya ci Iyon, da Abel-bet-ma'aka, da Yanowa, da Kedesh, da Hazor, da Gileyad, da Galili, da dukan ƙasar Naftali. Sa'an nan ya kwashe mutane zuwa bauta a Assuriya.
Ya ce, in kuma yi shela, in ce, “Ubangiji Mai Runduna ya ce wadata za ta sake bunƙasa cikin biranensa, zai kuma ta'azantar da Sihiyona, ya kuma zaɓi Urushalima.”
Sai na ce wa mala'ikan da ya yi magana da ni, “Mene ne waɗannan?” Shi kuwa ya ce mini, “Waɗannan su ne ƙahonin da suka warwatsa Yahuza, da Isra'ila, da Urushalima.”