Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Zakariya 1:1 - Littafi Mai Tsarki

1 A watan takwas a shekara ta biyu ta sarautar Dariyus, Ubangiji ya yi magana da annabi Zakariya, ɗan Berekiya, ɗan Iddo, ya ce,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 A wata na bakwai na shekara ta biyu ta mulkin Dariyus, maganar Ubangiji ta zo wa annabi Zakariya ɗan Berekiya ɗan Iddo.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Zakariya 1:1
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

wato, tun daga jinin Habila, har ya zuwa na Zakariya, wanda aka kashe tsakanin bagaden hadaya da Wuri Mai Tsarki. Hakika, ina gaya muku, duk za a bi shi kan mutanen wannan zamani.


Don alhakin jinin dukan adalai da aka zubar a duniya yă komo a kanku, tun daga jinin Habila adali, har ya zuwa na Zakariya ɗan Berikiya, wanda kuka kashe a tsakanin Haikalin da bagaden hadaya.


A rana ta huɗu ga watan tara, wato watan Kisle, a shekara ta huɗu ta sarautar sarki Dariyus, Ubangiji ya yi magana da Zakariya.


A rana ta ashirin da huɗu ga watan goma sha ɗaya, wato watan Shebat, a shekara ta biyu ta sarautar Dariyus, Ubangiji ya kuma yi magana da annabi Zakariya, ɗan Berekiya, ɗan Iddo.


An tsai da aikin Haikalin Allah a Urushalima, sai a shekara ta biyu ta sarautar Dariyus Sarkin Farisa.


A rana ta ashirin da huɗu ga watan tara a shekara ta biyu ta sarautar Dariyus, Ubangiji kuma ya yi magana da annabi Haggai ya ce,


A rana ta fari ga watan shida a shekara ta biyu ta sarautar sarki Dariyus, Ubangiji ya yi magana da annabi Haggai, cewa ya yi magana da Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, mai mulkin Yahuza, da Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist.


Ubangiji kuma ya yi magana da Haggai a rana ta ashirin da huɗu ga watan, ya ce,


a ranar ashirin da huɗu ga watan shida a shekara ta biyu ta sarautar Dariyus.


Haggai kuwa, da Zakariya ɗan Iddo, annabawa, suka yi wa Yahudawan da suke a Yahuza da Urushalima wa'azi da sunan Allah na Isra'ila wanda yake iko da su.


Ubangiji kuwa ya yi magana da annabi Haggai ya ce,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ