A lokacin keɓe garun Urushalima, sai aka nemo Lawiyawa a wurarensu duka don a kawo su Urushalima, su yi bikin keɓewa da farin ciki da godiya, da raira waƙoƙi da kuge, da garaya, da molo.
Sai Dawuda da dukan Isra'ilawa suka yi rawa da iyakar ƙarfinsu a gaban Allah, suna raira waƙoƙi suna kaɗa, garayu, da molaye, da ganguna, da kuge, suna busa ƙaho.
Sa'ad da ka isa Gibeya, wato tudun Allah, inda sansanin sojojin Filistiyawa yake, a nan kuma sa'ad da kake shiga garin, za ka tarar da ƙungiyar annabawa suna gangarowa daga wurin bagaden a kan tudu suna kaɗa garaya, da kuwaru, da sarewa, da molo, suna rawa suna sowa.
Sai ya zaunar da Lawiyawa a Haikalin Ubangiji, masu kuge, da molaye, da garayu, bisa ga umarnin Dawuda, da na Gad, maigani na sarki, da na annabi Natan. Gama umarnin daga wurin Ubangiji ya zo ta wurin annabawansa.
Dukansu tsohonsu ne yake bi da su da raira waƙoƙi, da kaɗa kuge, da molaye da garayu, cikin Haikalin Ubangiji, domin yin sujada. Asaf, da Yedutun, da Heman suna ƙarƙashin umarnin sarki.
Dawuda ya umarci shugabannin Lawiyawa su sa 'yan'uwansu mawaƙa su riƙa raira waƙa da murna, da kayayyakin bushe-bushe, da kaɗe-kaɗe, da molaye, da garayu, da kuge masu amon gaske.