7 Amma Ubangiji sarki ne har abada, Ya kafa kursiyinsa domin yin shari'a.
7 Ubangiji yana mulki har abada; ya kafa kujerarsa don shari’a.
Sa'an nan na ga wani babban kursiyi fari, da wanda yake a zaune a kai, sai sama da ƙasa suka guje wa Zatinsa, suka ɓace.
Amma ya ku ƙaunatattuna kada ku goce wa magana gudar nan, cewa ga Ubangiji kwana ɗaya kamar shekara dubu ne, shekara dubu kuma kamar kwana ɗaya ne.
Yesu Almasihu ba ya sākewa, shi ne a jiya, da yau, hakika har abada ma.
Ubangiji ya kafa kursiyinsa a Sama, Shi yake sarautar duka.
Amma kai, ya Ubangiji, sarki ne kai har abada, Dukan zamanai masu zuwa za su tuna da kai.
A gaskiya da adalci aka kafa mulkinka, Akwai ƙauna da aminci a dukan abin da kake yi.
Kafin a kafa tuddai, Kafin kuma ka sa duniya ta kasance, Kai Allah ne, Madawwami. Ba ka da farko, ba ka da ƙarshe.