Kada ku ɗauka daga cikin abin da aka haramta don zafin fushin Ubangiji ya huce, ya yi muku jinƙai, ya ji tausayinku, ya kuma riɓaɓɓanya ku ma kamar yadda ya rantse wa kakanninku,
Rana tana zuwa sa'ad da jama'a za su raira waƙa, su ce, “Ina yabonka ya Ubangiji! A dā ka yi fushi da ni, Amma yanzu kana yi mini ta'aziyya, ba za ka ƙara yin fushi da ni ba.
sai ka ji addu'arsu da roƙe-roƙensu, daga wurin zamanka a Sama, ka sa su yi nasara, ka biya musu muradinsu, ka gafarta wa jama'arka waɗanda suka yi maka zunubi.
Ka ƙarfafa jama'ar Urushalima. Ka faɗa musu sun sha wahala, ta isa, Yanzu kuwa an gafarta musu zunubansu. Na yi musu cikakken hukunci saboda dukan zunubansu.”
Ni Ubangiji na ce sa'ad da lokacin nan ya yi za a nemi laifi da zunubi a cikin Isra'ila da Yahuza, amma ba za a samu ba, gama zan gafarta wa sauran da suka ragu.