Ina addu'a matuƙa domin ceto ya zo ga Isra'ila daga Sihiyona! Sa'ad da Ubangiji ya sāke arzuta jama'arsa, Zuriyar Yakubu za su yi farin ciki, Jama'ar Isra'ila za su yi murna.
Ubangiji ya ce, “Ga shi, zan komar wa alfarwar Yakubu arzikinta, Zan kuma nuna wa wuraren zamansa jinƙai, Za a sāke gina birnin a kufansa, Fādar kuma za ta kasance a inda take a dā.
Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, “Nan gaba za su sāke yin magana a ƙasar Yahuza da biranenta a sa'ad da na mayar musu da dukiyarsu. “ ‘Ubangiji ya sa maka albarka, Ya wurin zaman adalci, Ya tsattsarkan tudu!’
Jimillar kayayyakin duka, na zinariya da na azurfa, dubu biyar da arbaminya (5,400). Sheshbazzar ya tafi da waɗannan kayayyaki duka tare da kamammun da suka komo daga Babila.