6 Su ne mutanen Edom, da Isma'ilawa, Da mutanen Mowab, da Hagarawa,
6 tentunan Edom da na mutanen Ishmayel, na Mowab da kuma na Hagirawa,
Zuriyar Ra'ubainu suka yi yaƙi da Hagarawa a kwanakin Saul. Suka ci Hagarawa, saboda haka suka zauna a ƙasar da take gabashin Gileyad.
Ka tuna, ya Ubangiji, da abin da Edomawa suka yi, A ranar da aka ci Urushalima. Ka tuna da yadda suka ce, “A ragargaza ta har ƙasa!”
Bayan wannan sai mutanen Mowab, da mutanen Ammon, tare da waɗansu daga cikin Me'uniyawa, suka zo su yi yaƙi da Yehoshafat.
Sai ya tattaro Amoriyawa da Amalekawa, ya je ya ci Isra'ilawa, ya mallaki birnin dabino, wato Yariko.
Sarakunan duniya sun yi tayarwa, Masu mulkinsu suna shirya maƙarƙashiya tare, Gāba da Ubangiji da zaɓaɓɓen sarkinsa.
Za a hallaka Mowab daga zaman al'umma, Domin ta tayar wa Ubangiji.