17 Ka sa a kore su, a razanar da su har abada, Ka sa su mutu, mutuwar ƙasƙanci!
17 Bari su kasance cikin kunya da taƙaici; bari su hallaka cikin wulaƙanci.
Ka sa a kori waɗanda suke ƙoƙari su kashe ni, a kunyatar da su! Ka sa waɗanda suke mini maƙarƙashiya su juya da baya, su ruɗe!
Ka sa kunya ta rufe maƙiyana, Ka sa su sa kunyarsu kamar riga.
Ka sa waɗanda suka ƙyaface ni a wahalata, A rinjaye su, su ruɗe. Ka sa waɗanda suke ɗaukar kansu sun fi ni, Su sha kunya da wulakanci!