Suka kama sarakunan Madayanawa biyu, Oreb da Ziyib. Suka kashe Oreb a kan dutsen Oreb, Ziyib kuwa suka kashe shi a wurin matsewar ruwan inabi na Ziyib a lokacin da suke runtumar Madayanawa. Sai suka kawo wa Gidiyon kan Oreb da na Ziyib a inda yake a gabashin Urdun.
Sai Zeba da Zalmunna suka ce, “Tashi da kanka, ka kashe mu, gama yadda mutum yake haka kuma ƙarfinsa yake.” Gidiyon kuwa ya tashi ya kashe Zeba da Zalmunna. Ya kwance kayan ado daga wuyan raƙumansu.