“Zan aukar wa mutane da wahala, Za su kuwa yi tafiya kamar makafi, Domin sun yi wa Ubangiji zunubi. Za a zubar da jininsu kamar ƙura, Namansu kuwa kamar taroso.”
Sai ya ce wa barorinsa, “Ku nemo mini wata mace mai duba domin in tafi wurinta in yi tambaya.” Barorinsa suka ce masa, “Ai, akwai wata mai duba a Endor.”
A yankin ƙasar Issaka da na Ashiru, Manassa yana da waɗannan wurare, Bet-sheyan da ƙauyukanta, da Ibleyam da ƙauyukanta, da mazaunan Dor da ƙauyukanta, da mazaunan Endor da ƙauyukanta, da mazaunan Ta'anak da ƙauyukanta, da mazaunan Magiddo da ƙauyukanta, da sulusin Nafat.
za su mutu da muguwar cuta. Ba za a yi makoki dominsu ba, ba kuwa za a binne su ba. Za su zama juji. Takobi da yunwa za su kashe su, gawawwakinsu za su zama abincin tsuntsayen sararin sama da na namomin jeji.”
Za a shimfiɗa su a rana, da a farin wata, da a gaban dukan rundunan sama, waɗanda suka ƙaunata, suka bauta wa, waɗanda suka nemi shawararsu, suka yi musu sujada. Ba za a tattara su a binne ba, amma za su zama juji a bisa ƙasa.
Ubangiji kuwa ya sa Barak ya yi kaca-kaca da Sisera, da karusansa duka, da rundunar mayaƙansa duka da takobi. Sisera kuwa ya sauka daga karusarsa, ya gudu da ƙafa.
Suka kama sarakunan Madayanawa biyu, Oreb da Ziyib. Suka kashe Oreb a kan dutsen Oreb, Ziyib kuwa suka kashe shi a wurin matsewar ruwan inabi na Ziyib a lokacin da suke runtumar Madayanawa. Sai suka kawo wa Gidiyon kan Oreb da na Ziyib a inda yake a gabashin Urdun.