Sa'an nan mala'ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji waɗansu muryoyi masu ƙara a Sama, suna cewa, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Almasihunsa, shi kuma zai yi mulki har abada abadin.”
“Domin haka ni Ubangiji na ce, Ku jira ni zuwa ranar da zan tashi in yi tuhuma. Gama na ƙudura zan tattara al'umman duniya, da mulkoki, Don in kwarara musu hasalata Da zafin fushina, Gama zafin kishina Zai ƙone dukan duniya.
Ubangiji ya ce, “Amma zan zo yanzu, Domin ana zaluntar masu bukata, Waɗanda aka tsananta musu kuma, suna nishi don zafi. Zan ba su zaman lafiya da suke nema!”